Home Labaru Fadin Gaskiya Ya Jawo Ake Hantarar Shugaban Majalisar Filato – Dan Majalisa

Fadin Gaskiya Ya Jawo Ake Hantarar Shugaban Majalisar Filato – Dan Majalisa

61
0

Wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta gabas da ta kudu Dachung Bagos, ya yi zargin cewa ana hantarar tsigaggen kakakin majalisar dokoki ta jihar Filato Ayuba Abok ne saboda fadin gaskiya.

Dachung Bagos ya bayyana haka ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai, inda ya ce an tsige kakakin majalisar ba bisa ka’ida ba, domin shida daga cikin ‘yan majalisar 24 ne su ka aikata hakan, wanda a cewar sa ya yi kasa da kashi 2 bisa 3 da kundin tsarin mulki ke bukata domin tsigewa.

Mista Bagos ya kara da cewa, an tsige kakakin majalisar ne da karfi da yaji, saboda ya fadi gaskiya a kan halin da tsaro ke ciki a jihar Filato.