Home Labaru Gwamna El-Rufai Ya Karɓi Rahoton Tsaro Na Shekara Ta 2021

Gwamna El-Rufai Ya Karɓi Rahoton Tsaro Na Shekara Ta 2021

127
0

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na Jihar Kaduna, ya karɓi rahoton bayanan tsaro na shekara ta 2021 daga Ma’aikatar Tsaro ta jihar.

Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya gabatar da rahoton a fadar gwamnati, yayin wani ƙwarya-ƙwaryan taro da ya samu halartar wasu kwamandojin rundunar sojin Nijeriya.

Rahoton tsaro na shekara ta 2020 dai ya nuna cewa, rikici ya kashe mutane 937 a jihar Kaduna, yayin da aka yi garkuwa da wasu dubu 1 da 972.

Kasancewar jihar Kaduna ta na fama da rikicin ƙabilanci a kudanci da hare-haren ‘yan bindiga, ɗaruruwan mutane ne ke rasa rayukan su duk shekara.