Home Labaru Uwargidar Atiku Ta Tsere Daga Kasar Bisa Barazana Ga Rayuwar Ta

Uwargidar Atiku Ta Tsere Daga Kasar Bisa Barazana Ga Rayuwar Ta

66
0

Uwargidan Tsohon mataimakin shugaban kasa Jennifer Abubakar, ta yi zargin cewa ta na fuskantar barazanar hallaka ta daga wasu makusantan shi, sakamakon rikicin sakin da ke tsakanin su yanzu haka.

A cikin wata sanarwar da ta raba wa manema labarai, Jennifer ta ce ta na ci-gaba da samun barazanar kisa daga makusantan Atiku Abubakar masu kokarin raba ta da kadarorin da ta mallaka.

Rahotanni sun ambato Jennifer na cewa, ta na fargabar rayuwar ta da ta ‘yayanta, saboda yadda masu tsaron lafiyar Atiku Abubakar ke yi mata barazana da kuma kiran ‘yan’uwan ta da kawayen ta da masu yi mata aiki tare da binciken kadarorin ta don a kwace su, baya ga sanya ido a kan wayar ta tare da ta kawayen ta da ‘yan’uwan ta.

Ta ce hakan ya sa ta fice daga ofishin ta na lauya, inda ta saida kadarorin ta tare da komawa kasar waje domin kare lafiyar ta, ta na mai cewa ita ta san ba ta aikata wani laifin da ya wuce bukatar saki daga Atiku Abubakar ba.