Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama Mai Kai Wa Bello Turji Makamai Da Wasu...

‘Yan Sanda Sun Kama Mai Kai Wa Bello Turji Makamai Da Wasu Mutane 36

108
0

Rundunar ‘yan sanda t a Jihar Sokoto, ta ce ta kama wasu ‘yan bindiga masu alaƙa da Bello Turji a wasu yankunan jihar.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi, muƙaddashin shugaban  ‘yan sanda na yankin Sokoto da Kebbi da Zamfara DIG Ahmed Zaki Gwandu, ya ce dakarun ‘yan sanda na musamman ne su ka gano sansanonin da ke da alaƙa da Bello Turji.

An dai kai samamen ne a ƙarƙashin jagorancin rundunar Operation Sahara Storm a ƙananan hukumomi uku na jihar, wadanda su ka hada da Rabah da Goronyo da kuma Illela.

Zaki Gwandu, ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai wani babban mai sama wa su Bello Turji makamai mai suna Musa Mohammed Kamarawa.

Tuni dai Karamawa ya amsa laifin sa a gaban ‘yan sanda, ya na sama wa ‘yan bindiga makamai, kuma akwai wani shugaban wata rugar Fulani a yankin Dege da ke jihar Filato, wanda ya ce ya daɗe ya na saida ma shi makamai.

Leave a Reply