Home Labaru Kiwon Lafiya COVID-19: Dokokin Fita Gida A Lokacin Dokar Hana Fita

COVID-19: Dokokin Fita Gida A Lokacin Dokar Hana Fita

719
0
An wajabta wa wadanda aka yi wa sassaucin dokar hana fita kiyaye matakan kariya daga cutar coronavirus.
Ka'idojin fita a jihohin Legas Ogun da Abuja lokacin dokar hana fita.

Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta dauki karin matakan dakile yaduwar cutar a jihohin Legas, Ogun da Abuja, inda Gwamantin Tarayya ta sanya dokar hana fita da nufin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

NCDC ta dauki matakan ne saboda sassaucin da dokar ta yi ga masu muhimman ayyuka da aka yi wa izinin fita a lokacin dokar.

Wuraren da aka yi wa sassaucin daga dokar hana fitar su ne motocin haya, bankuna, kantunan magani da masu sayar da kayan abinc.

Dokan wajabta wa wuraren wuraren da aka yi wa sassaucin, su samar da kayan wanke hannu ga ma’aikatansu da kwastomomi.

Za kuma su tabbatar an goge ko’ina da sinadarin kashe kwayoyin cuta akai-akai, sannan su tabbatar da bayar da isasshiyar tazarar tsakanin mutane.

A sanarwar da ta fitar, Cibiyar ta ce manyan shaguna na da damar budewa daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

Kasuwanni kuma an ba su damar budewa daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na rana.

Su kuma shagunan magunguna za su ci gaba da gudanar da aikinsu kamar yadda suka saba.

Ta bukaci masu fita saboda bukata da su dauki ragamar kula da lafiyarsu a duk sadda suka fita don kauce wa kamuwa da cutar.

Ta bukace su da su ba da tazarar mita biyu tsakaninsu da wasu a koyaushe, su guji cudanya da wasu, sannan su yawaita wanke hannayensu da ruwa da sabulu.