Home Labaru Gurfanar Da Yara Kanana: Gwamna Bala Muhammed Ya Bayyana Takaicinsa

Gurfanar Da Yara Kanana: Gwamna Bala Muhammed Ya Bayyana Takaicinsa

57
0
R
R

Al’umma a faɗin Najeriya na ci gaba da bayyana takaicinsu kan bidiyon yaran da aka gurfanar gaban kotu daga wasu jihohin arewacin ƙasar nan,

Yaran waɗanda gwamnati ta zarga da cin amanar ƙasa, sun bayyana a hotuna da bidiyo mabanbanta cikin yanayi na galabaita, ta yadda wasunsu ko tsayuwa ba sa iya yi.

Masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi tir da wannan mataki na kai yara ƙanana gaban kotu, tare da bayyana shi a matsayin cin zarafinsu.

Shima Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulƙadir Muhammad ya bayyana takaicinsa kan lamarin, wanda ya ce ya samu kiraye-kiraye daga sassa daban na ciki da wajen Najeriya kan lamarin.

Inda ya kara da cewa a matsayinsu na gwamnoni ya nuna musu akwai abin da ya kamata su yi wanda ba su yi ba na kula da yara. Idan aka yi kame ya kamata a riƙa duba yadda yaran da aka kama su ke a gidajen tsaro

Leave a Reply