Home Labaru Gurbacewar Muhalli Tamkar Gusar Da Al’umma Ne – Sentamu

Gurbacewar Muhalli Tamkar Gusar Da Al’umma Ne – Sentamu

240
0
Dakta John Sentamu
Dakta John Sentamu

Babban limamin cocin York na biyu mafi matsayi a kasar Ingila, ya bayyana gurbacewar muhalli a jihar Bayelsa da ke yankin Neja Delta a matsayin wani kisan kiyashi da ya shafi muhalli.

Dakta John Sentamu, ya ce ya kamata gwamnatin Nijeriya da al’ummar duniya su kara kaimi wajen rage barnar da malalar man fetur ke haddasawa a yankin.

Babban Limamin, wanda ke jagorantar wani kwamiti da ke bincike a kan illar ayyukan kamfanonin Mai a jihar Bayelsa, ya ce ba za su amince da halin-ko-in-kula daga kamfanonin ba, dole ne su dauki alhakin malalar da Mai ke yi daga kayan aikin su.

Dakta Sentamu, ya kuma zargi gwamnatin Nijeriya da kin daukar alhakin kare muhallin yankin Bayelsa.