Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Wata Cuta Ta Barke A Jihar Katsina, Ta Lashe Rayukan Mutane...

Annoba: Wata Cuta Ta Barke A Jihar Katsina, Ta Lashe Rayukan Mutane Da Dama

502
0

Wata cutar da ake zargin shawara ce, ta lashe rayukan mutane da dama a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Mazauna yankin sun ce, yawan wadanda su ka mutu ya kai 115, bayan gwamnatin karamar hukumar ta ce mutane 18 ne kacal su ka rasu a cikin makonni uku da su ka gabata.

Tsohon kansilan gundumar Kogware Sule Ibrahim, ya ce an fara samun barkewar cutar ne a gundumar Kogware kafin ta isa Unguwar-Sarka.

Ya ce, a cikin makonni uku da su ka gabata, sun kirga rashe-rashen mutane 112, tare da karin mutane 3 a cikin ranakun karshen makon nan, yayin da sakataren cibiyar lafiya ta yankin Dakta Shamsu Ahmad ya ce ana zargin cutar shawara ce.