Home Labarai Goodluck Jonathan Ya Samu Sabon Babban Aiki A Duniya

Goodluck Jonathan Ya Samu Sabon Babban Aiki A Duniya

322
0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya samu babban mukamin ]an kwamitin bada shawara na kasa da kasa a kungiyar Tarayyar Turai a kan Nahiyar Afirka da Gabas ta Tsakiya ECAM.

Jonathan dai ya zama shugaba na farko a yankin Hamadar Sahara, wanda ya zama shugaban hukumar ECAM ta kasa da kasa.

ECAM dai kungiya ce mai zaman kan ta da aka kafa da manufar ingantawa da kuma bunkasa dangantaka tsakanin kasashen Turai da Afirka da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da kuma Italiya da ke taka muhimmiyar rawa a ciki.

kungiyar, ta na alfahari da manya irin su tsohon Firayim Ministan Burtaniya Tony Blair da tsohon shugaban Hukumar Tarayyar Turai José Manuel Barroso da sauran wasu jiga-jigai da dama.

Kamar yadda yak e kunshe a takardar nadin Jonathan, shugaban hukumar ECAM Dr. Kamel Ghribi, ya ce kungiyar za ta yi farin cikin tarbar Goodluck Jonathan zuwa ofishin sa.

Leave a Reply