Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Janar Da Sojoji 7 A Jihar Taraba

‘Yan Bindiga Sun Kashe Janar Da Sojoji 7 A Jihar Taraba

36
0

Ana fargabar wasu ‘Yan bindiga sun kashe kwamandan sojoji na Bataliya ta 93 da ke Takum a jihar Taraba mai mukamin Birgediya Janar tare da wasu sojojin sa bakwai.

Shugaban karamar Hukumar Takum Shiban Tikari ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi karin haske a kan yadda lamarin ya auku ba.

Shiban Tikari, ya ce tuni shi da wasu jami’an tsaro sun shiga jeji, inda su ka yi kokarin gano gawarwakin sauran sojojin da ke tawagar Kwamandan.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, an samu aukuwar lamarin ne tsakanin Takum zuwa kauyen Tanti da ke kan hanyar zuwa Jalingo.

Majiyar ta ce Kwamandan ya na kan hanyar zuwa Jalingo ne lokacin da ‘yan bindigar su ka yi wa tawagar sa Kwanton-bauna.