Home Labarai Buhari Ya Umarci Ministocin Sa Masu Son Takara Su Yi Murabus

Buhari Ya Umarci Ministocin Sa Masu Son Takara Su Yi Murabus

17
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci ministocin da ke son tsayawa takara su yi murabus daga nan zuwa ranar 16 ga watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ya sanar wa manema labarai haka, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Daga cikin ministocin da lamarin zai shafa kuwa akwai ministan sufuri Rotimi Amaechi, da Ministan kwadago Chris Ngige, da Ministan shari’a Abubakar Malami, da kuma Minsitan Harkokin yankin Neja Godswill Akpabio.

Dukkan ministocin dai sun nuna sha’awar tsayawa takarar mukamai mabambanta, wadanda su ka hada da kujerar gwamna ko ta sanata ko ta shugaban ƙasa.