Home Labaru Arewa Maso Gabas: Sojoji Sun Yi Maganin Wasu ‘Yan Boko Haram A...

Arewa Maso Gabas: Sojoji Sun Yi Maganin Wasu ‘Yan Boko Haram A Garin Kollarum

853
0

Dakarun sojojin sama na Najeriya a karkashin rundunar Operation Lafiya Dole sun yi luguden wuta kan wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da su ka addabi Najeriya da yankin yammacin Afrika.

Sojojin sun ce dakarunsu sun kai wasu hare-hare akan mayakan Boko Haram a wani karamin kauye mai suna ne Kollarum da ke daf da tafkin Chad a jihar Borno.

An kai wadannan hare-hare ne a karkashin shirin  GREEN SWEEP na 3, inda aka dumfari wasu gidaje uku a wannan Kauye bayan an  sami labarin cewa mayakan Boko Haram su na yankin.”

Luguden wutan da jiragen su ka yi, ya rutsa da ‘yan ta’addan a inda aka yi masu mugun , sannan aka rusa gidajensu.

Air Vice Marshall S B Abubakar

Dakarun sojojin sama ta ce jami’an ta za su ci gaba da kokarin ganin sun yi maganin kaf mayakan ta’addan Boko Haram da ke addabar bayin Allah a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply