
Wata wutar gobara mai ban mamaki ta tashi da sanyin safiyar Talatar nan a babbar kasuwar birnin Onitsha na jihar Anambra.
Babbar Kasuwar dai ita ce kasuwa mafi girma a yammacin Afirka kuma ta na da dimbin ‘yan kasuwa, wadanda galibi masu shigo da kayayyaki ne su na kuma hada-hadar kayayyaki iri daban-daban.
Wata dan kasuwa Mista Barth Ifediora, ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Talata a wani sashe da aka fi sani da fadar White House.
Fadar White House ita ce ofishin shugabannin kasuwar, wanda gini ne mai hawa biyu da dakunan taro a hawa na daya da na biyu sai kuma shaguna a kasa.
Wata majiya ta ce, yankin da gobarar ta fi shafa shi ne bangaren shagunan da ke karkashin WhiteHouse, inda ake saida kayan yadidduka masu tsada.
You must log in to post a comment.