
Jami’yyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Katsina, ta na mai cewa tabbas za ta garzaya kotu domin neman hakkin ta.
Daraktan yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar PDP Mustapha Inuwa ya sanar da haka, a wani taron manema labarai a garin Katsina.
Idan dai ba a manta ba, bisa ga sakamakon zaben da hukumar zabe ta sanar, dan takarar jami’iyyar APC Dikko Radda ne ya lashe zaben da kuri’u dubu 859 da 892, yayin Yakubu Lado-Danmarke na jami’yyar PDP ya samu kuri’u dubu 486 da 620.
Mustapha Inuwa, ya ce sakamakon zaben ba shi ba ne zabin mutane, domin ba a yi zabe a jihar Katsina ba, don haka ba tare da wata shakka ba sun yi Allah wadai da sakamakon zaben da aka bayyana.
Ya ce an gudanar da zaben tare da tsoratarwa da cin zarafin mutane da sauran munanan aiyukkan da su ka saba wa dokar zabe, domin an hana magoya bayan PDP jefa kuri’a musamman a rumfunar zaben da aka san jami’yyar ta fi yawan magoya baya.
You must log in to post a comment.