Home Home Jam’iyyar LABOUR Ta Lashe Zaben Gwamnan Abia

Jam’iyyar LABOUR Ta Lashe Zaben Gwamnan Abia

10
0

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta sanar da Alex Otti na Jam’iyyar Labour a matsayin zababben gwamnan jihar Abia.

Tun farko dai hukumar zaben ta dakatar da sanar da sakamakon zaben ƙaramar hukumar Obingwa, saboda takaddamar da ta biyo baya da matsalolin da aka fuskanta a karamar hukumar.

Dan takarar Jam’iyyar Labour Alex Otti, ya doke abokin karawar sa na Jam’iyyar PDP Okey Ahiwe bayan ya kasance wanda ya fi samun kuri’u masu yawa. Alex Otti dai ya samu kuri’u dubu 175 da 467, yayin da Ahiwe na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 88 da 529.