Home Labaru Gobara Ta Hallaka Miji Da Mata Da Kuma ‘Yar Su A Kano

Gobara Ta Hallaka Miji Da Mata Da Kuma ‘Yar Su A Kano

306
0
Gobara Ta Hallaka Miji Da Mata Da Kuma ‘Yar Su A Jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane uku da su ka hada da wani magidanci da matar sa da kuma ‘yar su, sakamakon gobarar da ta afku a gidan su da ke Gayawa-Tsohuwa a karamar hukumar Ungogo.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jihar Kano Saidu Mohammed, ya ce wadanda su ka mutun sun hada da yarinya ‘yar shekaru biyu.

Ya ce sun samu kiran waya daga wani mutum mai suna Malam Mudassir Abdullahi, da misalin karfe 3:57 na safiyar Larabar da ta gabata, cewa gobara ta tashi a wani gida.

Mudassir Abdullahi, ya ce nan da nan su ka tura ma’aikatan su da kayan aiki domin kashe wutar, sai dai bayan an garzaya da mutanen zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad ne likitoci su ka tabbatar da mutuwar su.