Home Labaru Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore – Malami

Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore – Malami

238
0
Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore - Malami
Za Mu Girmama Kotu A Kan Sowore - Malami

Ministan shari’a Abubakar Malami , ya ce gwamnatin tarayya za ta yi biyayya ga umarnin kotu a kan sakin Omoyele Sowore da ke hannun hukumomin tsaro.

Ministan shari’a Abubakar
Ministan shari’a Abubakar

A farkon makon nan ne, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba hukumar tsaro ta farin kaya DSS umarnin sakin mawallafin jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore, sai dai yayin yanke hukuncin, kotun ta umarci Sowore ya bada fasfonsa na tafiye-tafiye. Hakan dai ya na zawa ne, bayan hukumar DSS ta janye karar da ta kai babbar kotun tarayya, inda ta nemi a cigaba da tsare Sowore bisa zargin shi da hannu a ta’addanci.