Home Labaru Dangote Ya Nuna Muradin Sadaukar Da Rabin Dukiyar Sa Ga Ayyukan Jinkai

Dangote Ya Nuna Muradin Sadaukar Da Rabin Dukiyar Sa Ga Ayyukan Jinkai

345
0
Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote

Shahararren dan kasuwa Aliko Dangote, ya ce ya na fatan ganin zuwan ranar da shi ma zai sadaukar da rabin dukiyar sa wajen ayyukan jin-kai, musamman bangaren inganta kiwon lafiya.

Dangote dai ya nuna muradin ganin shi ma ya bi sahun takwaran shi Bill da Melinda Gates, wajen gudanar da ayyukan jin-kai da dukiyar su.

Ya ce bai san irin gagarumin neman agajin da ake matukar bukata a Nijeriya ba sai da ya hadu da Bill Gates.

Aliko Dangote, ya ce haduwar da ya yi da Bill Gates ta sauya ma shi alkibla sosai, ta yadda ya kara ganin martaba da kima da kuma darajar dan Adam da ayyukan jin-kan al’umma.

Ya ce bai san akwai gagarumin kalubalen bukatar jin-kai a cikin al’umma ba, sai da Gidauniyar sa ta hada hannu da Gidauniyar Bill da Melinda.