Home Labaru Gidan Mari: Ana Cin Zarafin Masu Tabin Kwakwalwa A Nijeriya – HRW

Gidan Mari: Ana Cin Zarafin Masu Tabin Kwakwalwa A Nijeriya – HRW

235
0

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce dubban mutane masu lalular kwakwalwa ne aka rufe tare da cin zarafin su a gidajen marin da ta kai ziyara a Nijeriya.

Ta ce matsalar ba kawai ta shafi gidajen mari na masu zaman kan su ne ba, har ma da wadanda ke karkashin kulawar gwamnati.

Kungiyar, ta ce ta ziyarci cibiyoyin masu tabin kwakwalwa guda 28 mallakar musulmi da kirista a fadin Nijeriya a tsawon shekara guda, kuma ta gane wa idanun ta yadda ake daure su da mari.

Rahoton ya ce, ana tursasa wa masu lalurar gudanar da rayuwa cikin muhalli mai kazanta, kuma ta zanta da masu gudanar da gidajen marin a kan dalilin daure masu tabin hankali, inda su ka ce fargabar kada mutanen su tsere ko kuma illata wasu ne ya sa ake daure su.

Rahoton kungiyar dai ya na zuwa ne, yayin da jami’an tsaron Nijeriya ke kai samame gidajen mari a sassan jihohin Nijeriya, inda su ka kubutar da tarin wadanda wadanda iyayen su su ka kai da nufin gyaran tarbiya.