Home Labaru Kasuwanci Fasa-Kwauri: DPR Ta Janye Ba Gidajen Man Da Ke Kusa Da Iyakokin...

Fasa-Kwauri: DPR Ta Janye Ba Gidajen Man Da Ke Kusa Da Iyakokin Nijeriya Lasisi

634
0
Ma’aikatar Lura Da Arzikin Man Fetur, DPR
Ma’aikatar Lura Da Arzikin Man Fetur, DPR

Ma’aikatar lura da arzikin man fetur DPR, ta daina bada damar gina gidan mai tare da janye bada lasisi ga gidajen man da ke da kusancin tsawon kilomita 20 daga iyakokin Nijeriya har sai baba-ta-gani.

Hukumar DPR ta ce dalilin da ya sa ta yanke wannan shawara shi ne, taimaka wa muradun gwamnati na hana fasa-kwaurin man fetur a iyakokin Nijeriya.

Kakakin hukumar Paul Osu, ya ce bisa ga wannan sanarwa, su na ba dukkan wuraren ajiye man fetur da ‘yan kasuwar mai shawarar su daina kai man fetur wuraren har sai sun sake tuntubar su.

Wannan dai, ya biyo bayan umurnin hukumar hana fasa-kwauri ta Nijeriya, inda ta hana saida wa gidajen man da ke kimanin tsawon kilomita 20 daga iyakokin Nijeriya man fetur.