Home Labaru Boko Haram: Wayar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Babban Soji A Yobe

Boko Haram: Wayar Lantarki Ta Yi Ajalin Wani Babban Soji A Yobe

546
0

Wani jami’in Soji mai mukamin kaftin ya gamu da ajalin sa, bayan ya taka wayar wutar lantarki a jihar Yobe yayin gumurzu da mayakan Boko Haram.

Mazunan garin Damaturu dai sun yi gudun neman tsira yayin da Boko Haram su ka afka wa garin, amma cikin lokaci kadan dakarun sojin da ke bataliya ta 233 tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda su ka fatattake su.

A yammacin ranar Juma’ar da ta gabata ne, kakakin rundunar sojin Nijeriya ya tabbatar da mutuwar jami’in sojan, sai dai bai fadi sunnan shi ba domin rundunar ba ta sanar da iyalan mamacin ba.

Harin da Boko Haram su ka kai wa dakarun sojin a jihar Yobe ya auku ne, bayan rundunar ta sanar cewa wasu tubabbun ‘yan Boko Haram 24 sun mika wuya.

Rundunar ta yarda da tubar ‘yan ta’addan ne, bayan sun furta da bakin su cewa su ne ‘yan ta’addan da su ka buwayi mutane tun a shekara ta 2009.