Home Labaru Kamfanonin Sadarwa Sun Maida Wa Minista Pantami Martani A Kan Rage Kudin...

Kamfanonin Sadarwa Sun Maida Wa Minista Pantami Martani A Kan Rage Kudin Data

1294
0
Isa Ali Pantami, Ministan Sadarwa
Isa Ali Pantami, Ministan Sadarwa

Kamfanonin sadarwa na Nijeriya sun yi raddi a kan kiran ministan sadarwa Isa Ali Pantami, cewa a rage kudin Data cikin kwanaki biyar masu zuwa saboda ya yi tsada da yawa, inda su ka bayyana lamarin a matsayin abin da ya saba wa hankali kuma ba zai yiwu ba.

Kungiyar kamfanonin sadarwa ta Nijeriya ta bayyana wa manema labarai cewa, umurnin da ministan ya bada zai kori masu zuba hannun jari daga Nijeriya kuma hakan kama-karya ne.

Shugaban kungiyar Injiniya Gbenga Adebayo ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce bai kamata a rika yi wa ma’aikatar sadarwa kama-karya ba, saboda kada a kashe nasarorin da aka samu a bangaren sadarwa a shekarun baya.

A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamnatin tarayya ta umarci hukumar sadarwa ta Nijeriya NCC, ta tilasta wa kamfanonin sadarwar tare da samar da wani tsarin da zai tabbatar da rage farashin sayen ‘Data’ da ‘yan Najeriya ke yi, domin su na kokawa a kan tsadar ta.