Shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya nuna damuwa game da yadda ‘yan Majalisar wakilai da Sanatoci da dama su ka kasa samun nasarar cin zaɓen fidda-gwani.
Gbajabiamila, ya ce ba wani abu ya kada su ba sai tsarin da ya Deliget damar zaɓen wanda su ke so.
Ya ce yawancin waɗanda su ka kasa cin zaɓen fidda-gwanin ba al’ummar da su ke wakilta ne ba su son su ba, kawai wakilan zaɓen ‘yan takara ne su ka kada su.
Kakakin majalisar, ya bayyana tsarin a matsayin shirme ne, ya na mai cewa shi ya sa su ka yarda a bi tsarin ‘yar tinƙe kawai wajen zaɓen fidda gwani.
Gbajabiamila, ya yi kira ga ‘yan majalisar da ba za su sake tsayawa takara ba su cigaba da sadaukar da kan su wajen kare dimokraɗiyya a sauran shekara ɗaya da ta rage masu.