Home Labarai ‘Yan Sanda Dubu 17 Za Mu Tura Zaben Jihar Ekiti – Sufeta...

‘Yan Sanda Dubu 17 Za Mu Tura Zaben Jihar Ekiti – Sufeta Janar

89
0

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta ƙasa INEC, ta ce ta shirya gudanar da sahihin zaɓen gwamna a jihar Ekiti.

Da yak e jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a kan zabe da ya gudana a birnin Ado-Ekiti, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar sa za ta tabbatar da ganin kuri’ar mutane ce za ta ba duk wanda ya ci ba tare da aringizo ko magudi ba.

A ranar Asabar mai zuwa ne, masu zabe za su halarci rumfunan zaɓe a jihar Ekiti domin zaɓen gwamnan da zai jagoranci jihar na tsawon shekaru huɗu.

Daga cikin shirye-shiryen ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya, hukumar zaɓe ta haɗa taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin zabe, domin tattaunawa tare da ba juna shawara don ganin an yi zaɓen cikin kwanciyar hankali.