Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rade-radin cewa ya na shirin daukar dan’uwan sa Musulmi a matsayin abokin takara.
Tinubu ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a wajen gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar gabannin zaben gwamnan jihar Ekiti.
Bola Tinubu, ya nesanta kan sa daga jita-jitar da cewa, wadanda ke yada ta ba su kan tsarin dimokradiyya, kuma sun tsorata ne da nasarar da zai samu a babban zaben shugaban kasa na shekara ta 2023.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Tinubu ya ce tikitin mataimakin shugaban kasa na yankin arewa maso gabas ne kuma ma kiristoci ne, duk da dai ana kan tattaunawa game da wanda za a tsaida.
Bola Tinubu ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, babu kungiya ko wani mutum da zai iya tursasa mataimakin shugaban kasa a kan sa, amma zai zabi mataimakin shugaban kasa da kan sa kuma wanda zai amfani ‘yan Nijeriya.














































