Home Labarai Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 254 Da Ake Zargi...

Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 254 Da Ake Zargi A Najeriya

53
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 254 cikin mako biyu da take zargi da aikata miyagun laifuka.

Cikin wata sanarwar da mai Magana da yawun rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce rundunar ta samu gagarumin cigaba a yaƙi da aikata miyagun laifuka.

Ya ce bisa koƙarin da rundunar ‘yan sadan ta yi ta samu nasara kama mutum 254 da take zargi da aikata laifuka ciki har da ‘yan fashi 92 da masu garkuwa da mutane 153 tare da mutum tara da ake zargi da aiki da ƙungiyoyin asiri.

Sanarwar ta ce ‘yan sandan sun kuma kuɓutar da mutum 35 da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato ababen hawa bakwai da aka sace.

Haka kuma ‘yan sandan sun kuma ce sun ƙwato bindigogi 44 tare da harsasai kusan 477 da bindigogi daban-daban.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta ƙaddamar da samamen ne a jihohin Plateau da Cross River da Taraba da kuma birnin tarayyar Abuja.

Leave a Reply