Home Labarai Daukar Mataki: Gwamnan Filato Ya Sa A Kamo Wadanda Suka Kashe Makiyayi

Daukar Mataki: Gwamnan Filato Ya Sa A Kamo Wadanda Suka Kashe Makiyayi

151
0

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya umarci jami’an tsaro su zakulo wadanda suka kashe wani Bafulatani dan shekara 17 suka hallaka shanu 35 a Karamar Hukumar Barkin Ladi da ke jihar.

Daraktan yada labarai na gwamnan, Gyang Bere, ya ce, dole ne a hukunta wadanda suka yi wannan danyen aiki, tare da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Gwamna Mutfwang, ya yi Allah wadai da wannan abu na rashin bin doka da oda, ya kuma ce wannan mummunan aiki na maida hanun agogo baya ga kokarin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kowa da kowa ne a jihar.

Ya ce gwamnatin sa ba za ta ci gaba da hakuri ana yi wa jama’a kisan gilla ba.

Hakazalika ya bukaci shugabannin gargajiya da na addini, da matasa da na mata da duk wadanda abin ya shafa, su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki su tattaunawa, domin a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Leave a Reply