’Yan bindiga sun nemi a biya su kudin fansa da sabbin takardun Naira bayan sun yi garkuwa da mutum 46 a a kauyukan kananan hukumomin Funtua da Batsari na Jihar Katsina.
Da safiyar ranar Juma’ar da ta gabata ne Maharan kusan su 40 a kan babura, suka kashe mutum daya, tareda sace wasu 28, ciki har da mata da kananan yara a kauyen Karare da ke Karamar Hukumar Batsari.
Bayanai sunce “Daga cikin wadanda aka sace harda wasu dalibai daga kauyen Kokiya da ke hanyarsu ta zuwa Makarantar Sakandaren Je-ka-ka-dawo a kauyen.
Wani mazaunin garin ya ce yana asibiti lokacin da aka kai harin, amma ya tsallaka katanga ya tsere.
A daya harin kuma, ’yan bindiga sun far wa wani masallaci a kauyen Maigamji da ke kan Babbar Hanyar Funtua zuwa Dandume, inda suka bude wuta kan masu Sallar Isha’i.
Wani Ganau yace a yayin harin maharan sun harbi limamin da ke jan sallar da wani mutum daya, sannan suka sace mutum 18 daga masallacin a ranar Asabar.
Mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isa, yace suna gudanar da bincike domin tabbatar da adadin mutanen da abin ya rutsa da su.
You must log in to post a comment.