Home Labaru Gargadi: Ya Kamata Gwamnati Da AU Su Shiga Cikin Maganar Afrika Ta...

Gargadi: Ya Kamata Gwamnati Da AU Su Shiga Cikin Maganar Afrika Ta Kudu – Atiku

290
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bukaci hukuma ta dauki tsattsauran mataki game da zubar da jinin ‘yan Nijeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu.

Ya ce ya kamata gwamnatin kasar Afrika ta Kudu da kungiyar kasashen Afrika ta su dauki matakin gaugawa domin kawo karshen wannan lamari.

Atiku Abubakar, ya ce mummunan harin da ake kai wa ‘yan Nijeriya, ya na iya rusa dankon zumuncin da ke tsakanin manyan kasashen Afrika.

Shugaban kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu Adetola Olubajo, ya tabbatar da cewa an kai wa ‘yan Nijeriya hari a yankin Jeppestown da ke Birnin Johannesburg.