Shirye shirye sun yi nisa game da tafiyar shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Afirka ta kudu, domin kawo karshen hare-haren da ‘yan kasar ke kai wa ‘yan Nijeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama tare da asarar dukiyoyin su.
Ana sa ran shugaba Buhari zai yi tattakin ne a watan gobe, inda zai tattauna da shugaban kasar Afirka ta kudu da sauran mahukunta kasar game da cin zarafin da ‘yan kasar su ke yi wa baki.
A cikin wata sanarwar da ta fito daga ofishin jakadancin Nijeriya na kasar Afirka ta kudu, ta bukaci shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya kawo karshen wannan matsala, saboda Nijeriya ba za ta lamunta ba.
Jakadan Nijeriya a kasar Afirka ta kudu Kabiru Bala, ya ba ‘yan Nijeriya mazauna kasar tabbacin samun tallafin da ya kamata daga ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke Johannesburg da Pretoria.
Ya ce su na kira ga duk ‘yan Nijeriya da lamarin ya shafa, su je ofishin jakadancin su bada bayanin halin da su ke ciki.