Home Labaru Ilimi Taron Ilimi: Farfesa Yemi Osinbajo Osinbajo Ya Ziyarci Jihar Kano

Taron Ilimi: Farfesa Yemi Osinbajo Osinbajo Ya Ziyarci Jihar Kano

331
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci jihar Kano domin halartar wani taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki da za a gudanar a kan tursasa neman ilimi a matakin farko kuma kyauta domin al’ummar jihar Kano.

Farfesa Yemi Osinbajo, zai kuma kaddamar da wani katafaren aikin wutar lantarki mai amfani da hasken rana a jami’ar Bayero da ke Kano.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da tawagar sa, sun yi dakon jihar mataimakin shugaban kasar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da zummar yi ma shi kyakkyawar tarba.

Tawagwar gwamnan dai ta kunshi manyan kusoshin gwamnatin Kano da Sarakunan  gargajiya na masarautun Bichi da Karaye da Gaya da kuma Rano.

Yayin taron na kwanaki biyu da za a gudanar, ana sa ran kwararrun da kuma masana sa zu gabatar da jawabai a kan tsarin ilimin Tsangaya.