Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 6, Sun Kama 18...

Yaki Da Ta’addanci: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 6, Sun Kama 18 A Jihar Zamfara

551
0

Rundunar sojin Nijeriya ta kashe wasu ‘yan ta’adda 6, tare da kama wasu masu taimaka wa ‘yan ta’adda da bayanan sirri 18 ciki kuwa har da wani basarake a jihar Zamfara.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Kanar Sagir Musa ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce rundunar ta kai wa ‘yan ta’addan farmaki ne a ranar Asabar da ta gabata, a garuruwan Kirsa da Sunke da ke karamar hukumar Anka, da kuma karin garuruwan Doka da Matu da ke karamar hukumar Gusau.

Sanarwar ta ce, kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da bindigogi kirar AK47 guda 2, da karin wasu bindigogi kirar hannu guda 2, da babura da dai sauran su.

Leave a Reply