Home Labaru Dakile Ta’addanci: Yadda Haramta Sayar Da Gawayi Ya Jefa ’Yan Zariya Cikin...

Dakile Ta’addanci: Yadda Haramta Sayar Da Gawayi Ya Jefa ’Yan Zariya Cikin Kunci

6
0
Matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na hana safarar itace da gawayin girki ya sanya talakawa cikin damuwa.

Matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na hana safarar itace da gawayin girki ya sanya talakawa cikin damuwa.

A makon jiya ne gwamnatin jihar ta haramta safarar itace da gawayi da hawa babura a fadin jihar a matsayin matakan tsaro, lamarin da ya sanya akasarin al’ummar jihar cikin kunci, musamman talakawa.

Al’ummomi na kira ga Gwamna Nasiru El-Rufai da ya duba halin da talakawa ke ciki da kuncin rayuwa da matsin tattalin arziki ya kyale masu babura wadanda ba na haya ba, su yi aiki.

Masu babura da ba na haya ba, suna kai iyalansu makaranta suna zuwa gonakinsu sannan suna zuwa wajen aiki a kai.

Shi kuwa gawayi da itace sun kasance abubuwa masu sauki wajen girki ga talakawa amma a halin yanzu al’amarin ya wuce hankalin talakawa.

Wasu alumomin kuwa cewa suka yi, kamata gwamna ya sa jami’an tsaro su killace hanyoyin dazuka tare da kame duk wadanda ke shige da fice a cikin dazukan, amma ba a shigo cikin gari a takura jama’a ba yayin da har yanzu masu satar mutane ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.