Home Labaru Gargadi: Babu Abin Da Zai Iya Raba Nijeriya – IBB

Gargadi: Babu Abin Da Zai Iya Raba Nijeriya – IBB

234
0
Janar Ibrahin Badamasi Babangida, Tsohon Shugaban Kasa
Janar Ibrahin Badamasi Babangida, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahin Badamasi Babangida, ya bukaci ‘yan kabilar Igbo su cigaba da bada gudunmawa wajen gina Nijeriya, domin tabbatar wa jama’a cewa su na da muhimmanci ga kasa.

Babangida ya yi kiran ne, yayin da ya karbi bakuncin wakilan ‘yan kabilar Igbo daga jihohin arewa 19, wadanda su ka ziyarce shi a Abuja domin taya shi murnar cika shekaru 78 da haihuwa.

IBB ya ce, babu wani lungu da sako a Nijeriya da kasuwanci bai kai ‘yan kabilar Igbo ba, tare da bayyana su a matsayin masu tarbiyyar kasuwanci.

Janar Babangida ya kuma yi gargadin cewa, babu wani bambancin kabila ko addini ko kuma siyasa da zai sa Nijeriya ta rabu gida biyu.