Home Labaru Dawainiyar Iyali: Sarkin Anka Ya Gargadi Masu Karamin Karfi A Kan Auren...

Dawainiyar Iyali: Sarkin Anka Ya Gargadi Masu Karamin Karfi A Kan Auren Mata Sama Da Daya

245
0
Alhaji Attahiru Ahmed, Sarkin Garin Anka A jihar Zamfara
Alhaji Attahiru Ahmed, Sarkin Garin Anka A jihar Zamfara

Sarkin garin Anka a jihar Zamfara Alhaji Attahiru Ahmed, ya gargadi wadanda samun su bai taka kara ya karya ba a kan su kaurace wa auren mace sama da daya.

Basaraken ya yi wannan gargadi a fadarsa da ke garin Anka, inda ya ce aurace-auracen da ake kullawa tsakanin masu karamin karfi ke kara jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arziki da haddasa matsanancin talauci.

Ya ce  masu hangen nesa da dama sun fadakar tare da jan ankali, a kan auren mace sama da daya ga wadanda samun su ba ya da wani tasiri wajen kula da harkokin iyali da dawainiyar rayuwar su ta yau da kullum.

Alhaji Attahiru, ya ce ma’aikatan da samun su bai wuce Naira 15,000 ba a kowane wata, auren mace sama da daya ba nasu ba ne, domin ba za su iya daukar nauyin iyalan su ba.