Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bada umarnin janye belin tsohon shugaban kwamitin gyaran fanshon ma’aikata Abdulrasheed Maina.
A hukuncin da alkalin kotun mai shari’a Okong Abang ya zartar, ya bada umarnin a sake kamo Abdulrasheed Maina ‘duk inda aka gan shi.
Lauyan hukumar EFCC Mohammed Abubakar, ya ce an bada belin Maina a kan naira miliyan 500 da kuma mai tsaya ma shi, wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye naira miliyan 500 a kotu.
Hukumar EFCC dai ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhume-tuhume goma sha biyu da wani kamfani mai suna ‘Common Input Properties & Investment Limited’.
Bayan ta ba hukumomin tsaro izinin kamo shi, kotun ta ba hukumar EFCC damar gurfanar da Maina tare da tuhumar shi a kebance.
Kotun, ta ce za a saka kudin da mai belin shi ya biya a aljihun gwamnatin tarayya, saboda saba ka’ida da sharuddan da aka bada belin Maina a kan su.