Home Home Garambawul: Buhari Ya Amince Da Sake Fasalin Hukumar Yada Labarai Ta NBC

Garambawul: Buhari Ya Amince Da Sake Fasalin Hukumar Yada Labarai Ta NBC

131
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar sake fasalin kwamitin gudanarwa na hukumar yada labarai ta kasa NBC, biyo bayan karewar wa’adin tsohon kwamitin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar sake fasalin kwamitin gudanarwa na hukumar yada labarai ta kasa NBC, biyo bayan karewar wa’adin tsohon kwamitin.

A wata sanarwa da ya fitar, ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, ya ce Bashir Bolarinwa ne sabon shugaban kwamitin.

Ya ce daga cikin ‘yan kwmitin kuma, akwai wani wakilin hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da wakilin ma’aikatar yada labarai da al’adu da kuma shugaban hukumar ta NBC.

Lai Mohammed, ya ce ‘yan kwamitin su na wakiltar ra’ayoyi daban-daban kamar yadda dokar NBC ta tanada.

Sauran ‘yan Kwamitin sun hada da Wada Ibrahim da  Iheanyichukwu Dike da Adesola Ndu da Olaniyan Badmus da Bashir Ibrahim da Obiora Ilo da Ahmad Sajo da Bayo Erikitola.

Ministan ya kara da cewa, hukumar ta na da wa’adin tsawon shekaru uku ne.

Leave a Reply