Home Labaru Rikicin PDP: Godwin Obaseki Ya Gargadi Nyesom Wike Na Jihar Rivers

Rikicin PDP: Godwin Obaseki Ya Gargadi Nyesom Wike Na Jihar Rivers

225
0
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya yi wa gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike gargadin cewa, ya daina yi wa jam’iyyar PDP babakere domin ba gadon gidan su ce ba.

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya yi wa gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike gargadin cewa, ya daina yi wa jam’iyyar PDP babakere domin ba gadon gidan su ce ba.

Godwin Obaseki, ya ce mataimakin gwamnan jihar Edo Philip Shuaibu bai yi barazanar ficewa daga jam’iyyar PDP ba kamar yadda Wike ya ce.

Ya ce ba za ta yiwu Wike ya rika nuna halin babu wanda ya isa da shi a jam’iyyar PDP, dole sai yadda ya ke so kowa zai yi.

Obaseki, ya ce duk wani dan PDP ya na da hakki a jam’iyyar, don haka gwamna Wike ya daina hura hanci ya na yi wa mutane babakere kamar shi kaɗai ne ya isa a jam’iyyar.

Leave a Reply