Home Labaru Kabilun Irigwe Da Fulani Sun Yi Sulhu A Jihar Filato

Kabilun Irigwe Da Fulani Sun Yi Sulhu A Jihar Filato

16
0

Ƙabilun Irigwe da Fulani da ke zama a jihar Filato, sun amince su yi sulhu a tsakanin su domin samar da zaman lafiya da ci-gaban yankin su da karamar hukumar Bassa.

Idan dai ba a manta ba, karamar hukumar Bassa ta dade ta na fama da rashin zaman lafiya sakamakon rikici da rashin jituwa da aka rika samu tsakanin Fulani da ‘yan ƙabilar Irigwe.

Kabilun biyu su yi sulhun ne, a wani zama da su ka yi da sarakunan gargajiya da malaman addini, wanda kungiyar tattaunawa da wanzar da zaman lafiya ta DREP ta shirya.

Shugaban kungiyar kabilar Irigwe Daniel Geh da shugabanin kungiyar makiyaya Ronku Aka da Muhammad Nuru, sun rungumi juna domin nuna wa duniya sulhun da su ka yi.

Daniel Geh, ya ce kabilar Irigwe a shirye ta ke ta yi zaman lafiya da duk kabilun da ke karamar hukumar, ya na mai cewa tun asali su na zaman lafiya da Fulani, don haka zaman lafiya zai dawo idan sun ci gaba da zaman lafiya kamar da.