Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kara Kashe Mutane 16 A Jihar Zamfara

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kara Kashe Mutane 16 A Jihar Zamfara

295
0

A kalla mutane 16 ne suka mutu a wani hari da ‘yan ta’adda suka kai ranar Alhamis a kauyen Marke da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Mazauna kauyen sun ce ‘yan ta’addan sun isa garin ne a kan babura, sannan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, kana sun kora shanu kana kuma suka debi kayan abinci.

Wani mazaunin garin da aka tattauna da shi ya ce ‘yan ta’addan sun datse kan wasu, yayin da suka farke cikin wasu da wuka suka cire musu wasu kayan ciki. Sai dai Jaridar ta Daily Trust ta ce ta yi kokarin jin ta bakin mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfaran kafin wallafa labarin amman abin ya ci tura.

Leave a Reply