Home Labaru Fyade Ta Dubura: Kotu Ta Yanke Wa Malamin Makaranta Daurin Rai Da...

Fyade Ta Dubura: Kotu Ta Yanke Wa Malamin Makaranta Daurin Rai Da Rai

86
0

Kotun sauraren kararrakin cin zarafin mata da kananan yara
kanana da ke Ikeja a jihar Legas, ta yanke ma wani malamin
makaranta mai suna Bright Emelogu hukuncin daurin rai da
rai bayan an kama shi da laifin yi wa dan shekaru 14 fyade.

Alkalin kotun mai shari’a Abiola Soladoye, ya ce wannan mummunan abu da Emelogu ya aikata ya wuce gona da iri matuka.

Mai shari’a Soladoye, ya yanke hukuncin ne bisa ga bayanin da dalibin ya gabatar da sakamakon gwajin asibiti da aka gabatar a kotu.

Da yake bayani a kotun, dalibin ya ce malamin ya fara lalata da shi ne bayan ya fara koyar da shi idan aka tashi makaranta, ya na mai cewa idan malamin ya na koya ma shi karatu sai ya ce su shiga ban-daki, kuma ya kan tsorata shi cewa idan bai yi ba zai kada ni a jarabawa.

Alkalin kotun mai shari’a Soladoye, ya yi kira ga makarantu su matsa bincike a kan ma’aikata da malaman da su ke dauka domin koyar da yara.

Leave a Reply