Home Labaru Mun Samu Gawar Mutum 15, Shanu 2000 Sun Bace Da Kone Mana...

Mun Samu Gawar Mutum 15, Shanu 2000 Sun Bace Da Kone Mana Gidaje 78 A Filato – MACBAN

90
0

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN, ta ce an
kashe mutane 15 bayan wani farmaki da ake zargin an kai
masu a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, inda ta ce an
an kona gidajen Fulani 78, yayin da sama da shanu dubu 2 su
ka bace sakamakon farmakin.

Shugaban kungiyar na jihar Filato Nuru Abdullahi ya bayyana wa manema labarai haka a birnin Jos.

A ranar Asabar da ta gabata, kungiyar ta zargi jami’an tsaron jihar na ‘Operation Rainbow’ da kai wa yankin su hari tare da kunna masu wuta, zargin da rundunar ta musanta.

Nuru Abdullahi, ya ce a harin da aka kai wa kauyukan Mangu, sun gano gawarwaki 15 da aka kashe a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da Kimanin gidaje 78 su ka kone, sannan akalla Shanu dubu 2 har yanzu ba a gan su ba.

Ya ce akwai rahoton sirri da ke nuna cewa, akwai kwararrun ‘yan bindiga da aka dauka domin su fatattaki Fulunai daga ihar Filato da sunan rikici, don haka a halin yanzu su na kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo karshen abin da ke faruwa a karamar hukumar Mangu.

Leave a Reply