
Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Pankshin da Kanke-Kanam a majalisar wakilai Yusuf Adamu Gagdi, ya ce ya zuwa yanzu an tantance sama da mutane dubu hudu da su ka tsere wa tashin hankalin da ya faru a jihar Filato.
Yusuf Adamu Gagdi kara da cewa, yanzu haka an tabbatar da mutuwar sama da mutane cas’in, sannan fiye da mutane 50 daga cikin wadanda aka kashe a hare-haren ‘yan-bindiga a Kanam ya san su kuma sun san shi.
Dan Majalisa, ya ce sama da mutane dubu 4 sun tsere daga gidajen su sakamakon hare-haren na ranar Lahadin da ta gabata.
You must log in to post a comment.