
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sauya mazabar sa daga jihar Legas zuwa jihar Ogun.
Wata sanarwa da kakakin mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar, ya ce tun ranar 9 ga watan Janairun shekara ta 2021 ne Osinbajo ya sauya mazabar sa zuwa jihar sa ta asali wato Ogun.
Masu lura da harkokin siyasa dai, su na ganin matakin wata dabara ce ta kauce wa adawar da zai fuskanta a karkashin ‘yan jam’iyar APC ta jihar Legas zaben fidda gwani.
Tuni dai jamiyar APC reshen jihar Legas ta ce ta yanke shawara a kan wanda za ta mara wa baya a zabe mai zuwa kuma bai wuce Bola Tinubu ba.













































