Home Labaru Firgici: Ɗaliban Makarantar Salihu Tanko Da Aka Karbo Daga Hannun Ƴan...

Firgici: Ɗaliban Makarantar Salihu Tanko Da Aka Karbo Daga Hannun Ƴan Bindiga Na Kwance A Asibiti

81
0
Salihu Tanko Ismamiyya

‘Yan bidigar da suka sace daliban Islamiyyar nan ta Salihu Tanko da ke garin Tegina a jihar Neja sun sake su bayan shafe watanni uku suna tsare da su.

Rahotanni sun ce ko da yake babu alkaluman ko nawa ne daliban da aka saki,  saidai gwamnatin jihar ta Neja ta ce za ta yi karin bayani nan gaba da zarar an gama kirga su.

Kimanin dalibai 136 ‘yan bindigar suka sace lokacin da suka kai wa makarantar su hari a watan Mayun da ya gabata, amma wasu daga cikin su sun kubuta daga baya.

Mallam Abubakar Alhassan, shi ne shugaban Islamiyyar ta Salihu Tanko da ke garin na Tegina, kuma shi ne ya yi tattaki har zuwa yankin dajin Birnin Gwari, kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa ya zubar da hawaye saboda yanayin da ya ga yaran a ciki.

Malam Abukar ya ce yaran sun yi matsananciyar rayuwa a hannun ‘yan bindigar, har ta kai ga lokacin da ya karbe su ma wasu daga cikin su ba sa iya ko takawa da kafafun su, yayin da wasu kuma ke aman jini.

Ya kara da cewa kowa ya ga su ya san yunwa ta jigata su, domin wasun su na ta cin burodi, abin tausayi mai matukar tayar da hankali.