Home Labaru Kiwon Lafiya Cutar Korona: Adadin Wadanda Suka Kamu A Najeriya Ya Kai Dubu 189...

Cutar Korona: Adadin Wadanda Suka Kamu A Najeriya Ya Kai Dubu 189 Da 715

44
0
NCDC

Hukumar daƙile yaduwar cutuka a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 655 ne suka kamu da cutar korona a ranar Alhamis.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Rivers suke inda aka samu karin mutum 263 dauke da cutar, yayin da a Lagos aka samu mutane 217 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

Jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Alhamis su ne Rivers-263, Lagos-217, Oyo-128, Edo-45, Kwara-42, FCT-37, Ekiti-35, Ogun-13, Akwa Ibom-11, Imo-11, Bayelsa-10, Plateau-7, Delta-4 Kaduna-3, Benue-2, Niger-2, Sokoto-2, Abia-1, Ebonyi-1 Nasarawa-1

A jimillance adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 189,715, sai dai 169,626 sun warke. Akwai kuma mutum 2,298 da suka mutu.

A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau’in cutar korona da ake kira Delta a Najeriya, wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.