Wasu magoya bayan Bola Ahmed Tinubu, sun bude ofishin yakin neman zaben sa a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 a jihar Osun.
An dai bude ofishin yakin neman zaben ne a birnin Osogbo na jihar Osun, sannan an kafa babban allon tallata kudirin Tinubu a sakatariyar.
A jikin allon, an rubuta kalmomin da ke cewa Tinubu ba zai fasa takara a zaben shekara ta 2023 ba.
Ofishin
kuwa, ya na kallon ginin Gidan Oranmiyan, wato ofishin tsohon gwamnan jihar
Osun Rauf Aregbesola da ke kan hanyar Gbongan zuwa Ibadan a garin Osogbo.
You must log in to post a comment.