Home Labaru Fasa-Kwauri: Zan Sa Kafar Wando Daya Da Duk Jami’in Da Ke Samun...

Fasa-Kwauri: Zan Sa Kafar Wando Daya Da Duk Jami’in Da Ke Samun Fiye Da Albashin Sa – Hameed Ali

283
0
Hameed Ali, Shugaban Hukumar Yaki Da Fasa-Kwauri Ta Kasa
Hameed Ali, Shugaban Hukumar Yaki Da Fasa-Kwauri Ta Kasa

Shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya Kanar Hameed Ali, ya yi alkawarin fatattakar duk jami’in hukumar da ba zai iya dogaro da albashin sa ba, sannan aka kama shi da laifin tara dukiya ta hanyar da ba halas ba.

Hameed Ali ya bayyana haka ne, yayin da ya ke karrama jami’an hukumar da aka kara wa girma a Abuja.

Hukumar Kwastam dai ta kara wa jami’ai dubu 2 da 508 girma zuwa matsayi daban-daban, tare da nada wasu jami’an ta uku a matsayin a mataimakan shugaban hukumar.

Kanar Hameed Ali ya ja kunnen jami’an a kan rayuwa cikin wandaka da abin da ya fi karfin albashin su, matukar su na son ci-gaba da aiki da hukumar, inda ya ce kowane jami’i zai iya rayuwa a kan albashin da ake biyanshi idan ya tsara rayuwar shi da kyau.

Ya ce zai dauki mummunan mataki a kan duk jami’in da ya ce ba zai yi rayuwa da albashin sa ba, domin ya san ana ba su isassun kudaden da za su ishe su.