Home Labaru Hare-Haren Zamfara: Gwamna Bello Matawalle Ya Zargi Abdulaziz Yari

Hare-Haren Zamfara: Gwamna Bello Matawalle Ya Zargi Abdulaziz Yari

468
0
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamatin jihar Zamfara, ta dora laifin sabbin hare-haren da aka kai na baya-bayan nan akan tsohon gwamnan jihar Abdul-Azizi Yari.

Gwamna Bello Matawalle wanda ya ce ya yi sulhu da wadanda gwamnatin sa ta ke ganin sun addabi jihar, sannan ya zargi Abdulaziz Yari da yin zagon kasa ga sha’anin tsaro a jihar Zamfara.

Ya ce tsohon gwamnan ya na bakin ciki da zaman lafiyar da aka samu, wanda ya kasa magancewa tsawon shekaru 8 ya na kan mulki.

Matawalle ya yi zargin cewa, duk lokacin da Abdulaziz Yari ya ziyarci jihar Zamfara sai an kai hari, ya na mai barazanar cewa zai dauki mataki a kan tsohon gwamnan idan aka sake kai hari lokacin da ya shiga jihar Zamfara.