Home Labaru Cin Zarafi: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wanda Ya Ba Jami’an FRSC...

Cin Zarafi: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wanda Ya Ba Jami’an FRSC Kashi A Jihar Osun

195
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun, ta gurfanar da wani matashi mai suna Olasina Olanrewaju a gaban kotun majistare da ke Ile-Ife, bisa tuhumar sa da laifin lakada ma wasu jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa dukan tsiya.

Dan sanda mai shigar da kara Sufeto Sunday Osanyintuyi ya shaida wa kotun cewa, wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba da misalin karfe 8 na safe a shataletalen Ajebamidele da ke Ile-ife.

Ya ce wanda ake Olasina ya hada kai da wasu mutane biyu, wadan yanzu sun gudu, wajen dukan jami’an hukumar biyu.

Dan sandan ya kara da cewa, a ranar da lamarin ya auku, Taiwo Alonge da Bello Ishola su na gudanar da aikin su ne sanye da kayan sarki, yayin da Olasina da abokan shi biyu su ka yi amfani da waya wajen zane su, inda su ka ji masu rauni tare da kekketa masu riguna.

Alkalin kotun mai sharia Bose Idowu ta bada belin Olasina a kan kudi Naira 100,000, tare da mutane biyu da za su tsaya ma shi a kan Naira 100,000 kowannen su, sannan ta dage sauraren karar zuwa ranar 6 ga watan Disamba.